Bangaren kasa da kasa, Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi da ke kasar Labanon ya jaddada cewar haramtacciyar kasar Isra'ila barazana ce ga dukkanin kasashen yankin gabas ta tsakiya, don haka shafe ta daga kan doron kasa masalaha ce ga dukkanin kasashen yankin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, jagoran kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi da ke kasar Labanon ya jaddada cewar haramtacciyar kasar Isra'ila barazana ce ga dukkanin kasashen yankin gabas ta tsakiya, don haka shafe ta daga kan doron kasa masalaha ce ga dukkanin kasashen yankin baki daya.
A jawabinsa ga dubban jama'a a yayin taron gangamin ranar Qudus ta duniya a kudancin birnin Beirut na kasar Labanon a jiya Juma'a; Sayyid Hasan Nasrullahi ya jaddada cewa; dole ne al'ummar musulmin duniya su fi ba da fifiko kan batun 'yantar da Palasdinu saboda haramtacciyar kasar Isra'ila ba kawai barazana ce ga Palasdinu ba, domin cutar kansa ce mai yaduwa da take da mummunar hatsari ga dukkanin kasashen yankin gabas ta tsakiya.
Sayyid Hasan Nasrullahi ya kuma tabo makircin Amurka da 'yan koranta a yankin gabas ta tsakiya na kokarin kawar da hankular al'ummar musulmi daga kan matsalar Palasdinu ta hanyar kunna wutar rikici a tsakanin musulmi domin yahudawan sahayoniyya su samu damar ci gaba da aiwatar da ayyukan zalunci da wuce gona da iri kan Palasdinawa.
Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ya kara da jaddada matsayin kungiyarsa na ci gaba da gwagwarmayar kare al'ummar Palasdinu da ake zalunta da alkiblar musulmi na farko wato masallacin Qudus mai alfarma.
1267059