IQNA

Jagora ya gana da wasu daga cikin manyan jami'an gwamnati

13:37 - August 03, 2013
Lambar Labari: 2570315
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da manyan jami'an bangarori daban-daban na gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda yayi karin haske kan batutuwa daban-daban da suka shafi kasar Iran da alakarta da sauran kasashe bugu da kari kan abubuwan da ya kamata a ba su muhimmanci matuka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya fara jawabin nasa ne da godiya ga Allah Madaukakin Sarki saboda samun damar ganin wani watan Ramalana mai alfarma na daban da kuma samun damar amfanuwa da irin albarkokin da ke cikinta inda ya ce: Daya daga cikin nauyin da ke wuyan ‘yan'adam shi ne kara kan-kan da kai da kusaci da Allah bayan duk wata nasara da falala ta Ubangiji da ya samu.
Yayin da yake ishara da taimakon Ubangiji daya bayan daya da al'ummar Iran suke ci gaba da samu, Jagoran cewa ya yi: Daya daga cikin falaloli da taimako na Ubangiji na baya-bayan nan ga kasar Iran shi ne taimako mai girma na irin gagarumar fitowar da al'umma suka yi a lokacin zaben shugaban kasar da aka gudanar, wanda a sannu a hankali tasirin irin wannan gagarumar fitowa zai ci gaba da bayyana a bangarori daban-daban.
Ayatullah Khamenei ya bayyana haduwar irin wannan gagarumar fitowa ta siyasa da al'ummar Iran suka yi da kuma shigowar watan Ramalana a matsayin wata nasara da dacewa ta Ubangiji yana mai cewa: Watan Ramalana wanda wata ne na rahama da gafara ta Ubangiji sannan kuma ga irin albarkoki da addu'oi da ayyuka na ibadu da ke cikinsa, wani share fage ne na karin kan-kan da kai ga Allah Madaukakin Sarki. A saboda haka wajibi ne kowa da kowa ya yi kokarin amfanuwa da wannan gagarumar dama da aka samu.
Jagoran ya bayyana godiya ga Allah Madaukakin Sarki cikin tsanani ko kuma jin dadi a matsayin lamarin da ke lamunce kamala ga dan'adam yana mai cewa: Wajibi ne irin wadannan komawa ga Ubangiji ta zamanto ta share fagen samar da ayyukan da babu tsaiko da yanke kauna cikinsu.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana hakuri da dogaro da Allah a matsayin laziman irin wannan aikin yana mai cewa: Hakuri yana nufin tsayin daka, gwagwarmaya da kuma rashin mancewa da manufar da aka sa a gaba. Dogaro da Allah kuwa yana nufin neman taimakon Allah bayan an yunkura da kuma yin wani abu a kas.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da rawar da hakuri da dogaro da Allah suke takawa cikin ayyuka na daidaiku da kuma wadanda suka shafi shafi gudanar da kasa, Jagoran ya yi ishara da wasu abubuwa wadanda suke da tasiri cikin wadannan abubuwa guda biyu yana mai cewa: Batu na farko shi ne zaban matsayar da ta dace da kuma yin dukkanin abin da za a iya wajen kiyaye hakan.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Matukar dai aka yi kuskure wajen zaban matsayar da ta dace, to kuwa aiki da kokari ba wai kawai ma ba za su kai mu ga sakamakon da muke so ba ne, face ma za ta nesanta mu ne daga manufar da muka sa a gaban.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da jawabin da ya yi a wajen bikin tunawa da zagayowar ranar rasuwar marigayi Imam Khumaini (r.a) na wannan shekarar da aka gudanar wajen bayyanar da mahangar da ta dace a rika inda ya ce: Kamar yadda na fadi a wancan ranar, mahangar da ta dace sannan kuma ingantacciya ta wannan juyin da kuma kasar nan ita ce wacce ta yi daidai da koyarwar marigayi imam, sannan kuma wadannan koyarwar a fili suke da ba sa bukatar wani bincike.
Jagoran ya bayyana marigayi Imam Khumaini a matsayin masani sannan kuma mai hangen nesa inda yace: Koyarwar Imam wadanda suke cikin maganganu, rubuce-rubuce da kuma ayyukan da ya bari cikin kuwa har da wasiyyarsa, a fili suke a gaban masana, jami'ai da dukkanin al'umma, duk kuwa da cewa a wasu lokuta a kan sami wasu suna yi musu fassarar da ke ciki da kura-kurai.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar wajibi ne a bayyanar da irin wadannan koyarwa ta Imam cikin siyasar kasa da kuma hanyoyin gudanarwa na kasa.
Yayin da ya koma ga lamurran cikin gida na kasar Iran kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da kusatowar lokacin mika mulki ga sabuwar gwamnati a kasar Iran yana mai cewa: Shigowar sabbin jami'ai, sabbin mahanga da zauki na aiki a fagen gudanar da kasa, wata gagarumar dama ce da wajibi ne a yi amfani da ita.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Alhamdu lillahi a koda yaushe lokacin mika mulki a Iran ya kasance wani lokaci ne na farin ciki da kwanciyar hankali in ka cire shekara ta 2009 lokacin da wasu suka aiwatar da gagarumin kuskure a kasar nan.
Jagoran ya kara da cewa: wajibi ne sabbin jami'an da za su shigo fage su yi kokarin amfanu da ayyuka masu kyaun da aka gudanar a baya wajen ciyar da kasar nan gaba. Har ila yau kuma Jagoran ya yi ishara da irin ayyuka masu girman gaske da gwamnati mai ci yanzu ta gudanar don haka ya kirayi gwamnati mai zuwan da ta yi amfani da wannan damar wajen kara karfafa ayyukanta.
A jawabin nasa dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da wasu batutuwa guda bakwai da suka shafi kasar Iran a halin yanzu inda yayi ishara da bigiren da Iran take, irin tsohon tarihi da kyawawan al'adun da take da shi bugu da kari kuma kan irin dimbin arzikin albarkatun kasa da Allah ya yi wa kasar ga kuma kwarewa ta dan'adam a matsayin uku daga cikin wadannan batutuwa guda bakwai da kasar Iran take da su. Jagoran ya bayyana cewar: Tsawon karnoni biyu zuwa ukun da suka gabata kasar Iran ta fuskanci matsaloli da gagarumar cutarwa sakamakon mulkin kama karya na cikin gida da kuma makirce-makircen makiya daga waje, wanda wajibi ne a yi la'akari da wadannan abubuwan.
Jagoran ya yi karin haske dangane da yunkure-yunkuren da al'ummar Iran suka yi tsawon tarihi da suka hada da yunkurin kundin tsarin mulki, yunkurin ‘yan kasantar da kamfanonin man fetur da kuma juyin juya halin Musulunci da ya faru a kasar inda ya ce: yunkurin ‘yan kasanci na kundin tsarin mulki da ‘yan kasartar da kamfanonin mai dai sun sha kasha, to amma juyin juya halin Musulunci ya kai ga nasara ta hanyar kafa Jamhuriyar Musulunci wanda yake a matsayin mayar da martani da kokarin lalata al'adu da ci gaban al'ummar Iran da makiya suke yi.
Ayatullah Khamenei ya bayyana irin nasarorin da Iran ta samu a fagage daban-daban na siyasa da tattalin arziki da ilimi da al'adu a matsayin lamari na shida a wannan fagen. Kamar yadda kuma ya bayyana irin tsarin demokradiyya na addini da ke gudana a kasar Iran a matsayin lamari mai matukar muhimmanci cikin tsarin gudanarwa na kasar Iran.
Batu na karshe da Jagoran ya yi ishara da shi shi ne irin gagarumar kiyayya da kuma makirce-makircen da makiya suke kullawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda ya ce: Ma'abota girman kan duniya da wasu daga cikin ‘yan siyasar kasashen yammaci da wasu jami'an wasu gwamnatocin wannan yankin sun bude wani gagarumin fagen na adawa da kiyayya da al'ummar Iran da ya zuwa yanzu babu wata al'ummar da ta taba fuskantar irin wannan kiyayyar.
Don haka Jagoran ya ce: Don ci da bin wannan tafarki na ci gaba da al'ummar Iran suka kama wajibi ne a yi riko da hakuri da kuma dogaro da Allah da kuma tsayin daka a gaban makiya bugu da kari kan gina kasa.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Bai kamata jami'an gwamnati su ji tsoro ko fargabar barazana da fushin makiya a fagagen siyasa, tattalin arziki da farfaganda ba.
Batu na karshe da Jagoran ya yi magana kansa shi ne batun alaka da kasashen duniya. Dangane da wannan batun, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Mu dai tun ranar farko mun yi amanna da kyautata alaka da kasashen duniya kuma har ya zuwa yanzu ma mun yi amanna da hakan. To amma abin da ke da muhimmanci wajen alaka da duniya shi ne fahimtar bangaren da ake fuskanta din da kuma manufar da ya sa a gaba. Saboda kuwa idan har ba mu fahimce shi ba, to kuwa za mu kasa.
Jagoran ya ci gaba da cewa: A yayin alaka da duniya, bai kamata mu yi watsi da kuma rufe ido kan ayyukan da makiya suka gudanar ba, ta yadda ko da ma saboda wata maslaha, za mu iya gabatar musu da su.
Har ila yau kuma yayin da ya ke magana kan maganganun da Amurkawa suke yi na tattaunawa da Iran, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: A farko-farkon shekarar nan na fadi cewa ni dai ba na da wani kyakkyawan fata dangane da tattaunawa da Amurka, duk kuwa da cewa a shekarun baya ma ban hana tattaunawa da Amurka da aka yi kan wasu batutuwa irin su kasar Iraki ba.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Amurkawa dai ba abin yarda ba ne sannan kuma ba masu amfani da hankali ba ne, haka nan kuma ba su da gaskiya cikin mu'amala da ayyukansu.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Abubuwan da suka yi cikin ‘yan watannin baya-bayan nan na kara irin wannan mahanga da cewa su din nan ba abin yarda da kuma fata mai kyau ba ne.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Kwarewa cikin mu'amala da duniya ita ce za a iya ci gaba da riko da tafarkin da aka rika, ba tare da cewa wanda ake tinkara din ya hana ku gudanar da ayyukanku ba. Idan kuwa har alaka da kasashen duniya za ta mai da mu baya daga tafarkin da muka rika, to hakan hasara ce.
Kafin jawabin Jagoran sai da shugaban kasar Iran Dakta Mahmud Ahmadinejad ya yi karin haske kan irin ayyukan da gwamnatinsa ta aikata tsawon shekaru takwas din da suka gabata wanda ya ce gwamnatin tasa ba za ta sami damar cimma wadannan ayyuka ba in ba don taimako na Ubangiji, goyon bayan da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ba wa gwamnatin da kuma hadin kan al'ummar Iran ba. Don haka ya gode wa Jagoran kan irin goyon bayan da ya ba wa gwamnatin tasa da kuma yin alkawarin ci gaba da gudanar da ayyuka da kuma hidima wajen ciyar da kasar Iran da kuma juyin juya halin Musulunci gaba.


1267131

captcha