IQNA

Zababen Shugaban Iran Dr Hassan Rohanni Ya Kama Aiki

9:42 - August 04, 2013
Lambar Labari: 2570578
Bangaren siyasa, sabon Shugaben Jamhuriya Misilimci ta Iran Dr Hassan Rohani wanda ya lashe zabubukan kasar na Ran 14 ga watan Yuni ya kama aiki sa na shugabancin kasar a hukumance Yau Asabar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a wani jawabi daya gabatar wurin bikin kama aikin na sa shugaba Hassan rohani yayi alkawalin maida hankali wajen batun daya shafi cire ma kasar sa jerin takukunmi marasa tushe da kasashen Yamaci suka kakabawa kasar ta Iran bisa batun makamashin nukuliyar ta na zamen lafiya.
A hanu daya kuma Sabon shugaba Cheik Rohani yayi alkawalin farfado da tatalin arzikin kasar, inganta hulda sakanin kasar ta Iran da sauran kasashen duniya dama kare duk hurimin da kasar sa ciki da waje.
Dr Hassan Rohani dan shekaru 64 da haifuwa zai maya gurbin sohon shugaba Ahmedi Nejad a wa'adin shugabacin kasar na shekaru hudu, wanda kuma zai kasance shugaban jamhuriya Misilimci ta Iran na 7.
Bikin kama aikin sabon shugaba Rohani daya gudana yau a birnin Teheran ya samu halartar jagoran Juyin Juya halin Misilmci Ayatolah Alihamnei tareda halartan duban wakilan kasashen duniya ciki harda sohon jakaden hulda da kasashen wajen a kungiyar taraya Turai Mr Javier Solana.
Gobe ne dai Shugaba Hassan Rohani zai yi ransuwar kama aiki a gaban majalissar Dokokin kasar .
1267702

captcha