IQNA

Kotu A Masar Ta Bada Umurnin Ci Gaba Da Tsare Hambararren Shugaban Kasar Muhammad Morsi

13:45 - August 13, 2013
Lambar Labari: 2574663
Bangaren kasa da kasa, Kotu a kasar Masar ta bada umurnin ci gaba da tsare hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi na wasu karin kwanaki goma sha biyar, alkalin kotun da ke gudanar da bincike kan tuhumce-tuhumcen da ake yi wa hambararren shugaban kasar Masar Muhmmad Morsi a yau Litinin ya sake bada umurnin ci gaba da tsare shi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Tun bayan da sojoji a kasar Masar suka kifar da gwamnatin Muhammad Morsi a ranar uku ga watan Yulin da ya gabata suka masa daurin talala a gidansa, sannan a ranar 26 ga watan Yulin wata kotu a kasar ta bada umurnin tsare hambararren shugaban a wani waje da ba a sanar ba kan tuhumce-tuhumce da ake yi kansa da suka hada da game baki da kungiyar Hamas domin aiwatar da ayyukan barna a cikin kasa, kai hari kan ofisoshin 'yan sanda da na soji, kai farmaki kan gidan kurkuku gwamnati da lalata ginin gami da bunka masa wuta.

Magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammad Mursi suna ci gaba da zaman dirshan a birnin Alkahira, duk kuwa da irin matakan da mahukuntan kasar suka ce za su dauka na yin amfani da karfi wajen kawo karshen wannan zaman dirshan da suke yi a dandalin Rabiat Aladwiyyah da kuma Nahda, matukar dai ba su bar wuraren salun alun ba.

Firayi ministan rikon kwaryar kasar ta Masar ya bayyana cewa bas u da nufin murkushe magoya bayan kungiyar ‘yan uwa musulmi ko yin waje rod da su daga harkokin siyasar kasar ba, amma wajibi ne magoya bayan kungiyar tare da jagororinsu su mutunta doka, kuma hakkin ma’aikatar harkokin cikin gida ne ta dauki dukkanin matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron cikin gida tare da kare rayukan al’umma da dukoyoyinsu.

Tun bayan kifar da Morsi a farkon watan Yulin da ya gabata, kasar ta Masar ta shiga danbarwar siyasa, inda yanzu haka wasu mutane suke ci gaba da kaddamar da harehare da manyan makamai kan sojoji da rundunar ‘yan sanda ayankin Sina, lamarin da mataimakin shugaban kungiyar ‘yan uwa musulmi Khairat Shatir ya bayyana shi da cewa ba zai kawo karshe ba har sai an dawo da Morsi a kan shugabancin kasar Masar.

1271776



captcha