Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babban malamin sunna na kasar Lebanon a hukumance sheih Rashid Qabbani ya bayyana cewa, haramtacciyar kasar Isra’ila ce kawai ta amfana da aharin da aka akia birnin Beirut na kasar Lebanon a unguwar da magoya bayan kungiyar Hizbullah suka fi yawa da nufin kara kawo riki a kasar tsakanin mabiya mazhabobi da addinai da ke zaune da juna lafiya.
A bangare guda kuma Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Labanon ya bayyana harin da aka kai kudancin kasar Labanon da cewar harin ta'addanci ne mai hatsari.
A jawabin da ya gabatar a bikin tunawa da gagarumar nasarar da kungiyar Hizbullahi ta samu a yakin kwanaki 33 da ta yi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin watan Yulin shekara ta 2006 a garin Aita-Sha'ab da ke kudancin kasar Labanon a yau Juma'a; Sayyid Hasan Nasrullahi ya bayyana cewar ga dukkan alamu masu dauke da ra'ayin kafirta musulmi ne suka aiwatar da harin ta'addancin da aka kai kudancin birnin Beiruit a jiya Alhamis da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 22 tare da jikkata wasu 330 na daban.
Sayyid Nasrullahi ya jaddada cewar ba mu kwakonton cewar akwai hannun cibiyoyin leken asirin Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila gami da gwamnatocin da suke 'yan koransu na yankin gabas ta tsakiya a shirya makircin kai harin.
Babban sakataren kungiyar ta Hizbullahi ya kuma fayyace cewar masu dauke da ra'ayin kafirta musulmi suna kashe jinsin bil-Adama ne ba tare da bambance tsakanin dan Shi'a ko Sunna ba ko kuma tsakanin musulmi da kirista musamman idan aka yi lakari da kashe-kashen gillar da suke yi a kasashen Siriya, Somaliya da Iraki, kuma mutane da aka ba su umurnin rusa yankin gabas ta tsakiya baki daya.
Har ila yau Sayyid Hasan Nasrullahi ya jaddada cewar gagarumar nasarar da kungiyarsa ta samu a kan gwamnatin h.k.Isra'ila a yakin watan Yulin shekara ta 2006 nasara ce da ta rusa gagarumin shirin yahudawan sahayoniyya na kokarin mamaye yankin gabas ta tsakiya tare da shimfida bakar siyasarsu ta zalunci a kan al'ummar yankin.
1274395