Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Majiyar shari'ar kasar Masar ta bayyana cewar tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak ya gurfana a gaban kotu a jiya Lahadi bayan sakinsa daga gidan kurkuku a ranar Alhamis da ta gabata, inda a halin yanzu yake fuskantar shari'a kan zargin hannu a kashe masu gudanar da zanga-zangar lumana a lokacin boren neman kawo karshen gwamnatinsa ta kama karya a shekara ta 2011.
Majiyar ta kara da cewar daga cikin mutanen da suka gurfana a gaban kotun a jiya Lahadi sun hada da 'ya'yayen tsohon shugaban kasar guda biyu da kuma tsohon ministan harkokin cikin gidan Masar gami da wasu manyan jami'an tsaron kasar guda shida.
Tun a cikin watan Yunin shekara ta 2012 ne wata kotu a kasar Masar ta zartar da hukuncin daurin rai da rai a gidan kurkuku kan tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak, sannan a cikin wannan wata na Ogusta babbar kotun daukaka kara a kasar ta Masar ta bada umurnin sakinsa tare da sake gudanar da wata sabuwar shari'a kan zarge-zargen da ake yi kansa.
1277995