Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Yayin da duniya take jiran jawabin shugaba Obama kan rikicin Siriya, daga karshe dai shugaban kasar na Amirka, ya yanke shawarar cewa zai kai farmakin soja ta sama, amma babu sojan kasar Amirka na kasa da za su je cikin Siriya don yaki, don haka Obama ya ce farmakin takaitacce ne.
Sai dai shugaba Obama ya ce duk da cewa yana da izinin dokar da ta ba shi karfin kai harin soja, amma ya yanke shawarar kai batun gaban majalisar dokoki domin ta yanke shawarar. A wani abin da ya shafi batun Siriya, jami'an Majalisar Dinkin Duniya da ke binciken amfani da makamai masu guba sun isa kasar Hollande bayan kammala bincike a Damaskus, za su isa cibiyar bincike ta MDD da ke birnin Hague, inda za su dauki kwanaki suna binciken shaidar da suka samu, kan yin amfani da makamai masu guba, Jami'an binciken sun bayyana cewar binciken na su yana bukatar lokaci.
A wani labarin kuma Majalisar dokokin Birtaniya ta ki amincewa da kokarin da firaministan David Cameron na kasar yake yi na shiga sahun Amurka da wasu kawayenta da suke ta kada kugen yaki da nufin kai wa kasar Siriya hari saboda zargin amfani da makamai masu guba da har ya zuwa yanzu sun gagara tabbatar da hakan.
David Cameron dai ya gagara samun goyon bayan kai harin sojin ne da ya bukata daga wajen majalisa bayan da 'yan majalisar suka ki amincewa da wannan bukata a wata zama da suka yi a jiya.
Jim kadan bayan kada kuri'ar, inda 'Yan majalisan Birtaniya 285 ciki har da 'yan jam'iyyar Cameron ne suka ki amincewa da bukatar, firayi ministan na Birtaniyya ya sanar da aniyarsa ta girmama wannan kuduri da majalisar ta dauka, kamar yadda sakataren tsaron Birtaniyan ma dai ya sanar da cewa kasarsa ba za ta shiga cikin wannan yakin ba.
Tun kafin zaman majalisar dai al'ummomin Birtaniyan suke ta zanga-zangogin nuna rashin amincewarsu da wannan yakin suna masu kiran gwamnatin kasar da kada ta bari Amurkawan su sake yaudararta kamar yadda suka yi a lokacin yakin da suka kai wa kasar Iraki a shekara ta 2003 da kawar da gwamnatin Saddam Husain da zargin cewa yana da makaman kare dangi amma daga baya kuma ta bayyana cewa babu gaskiya cikin wannan zargi da Amurkan ta yi wa gwamnatin ta Iraki.
1280870