IQNA

Manufar Barazana Ga Syria Ita ce Kare Haramtacciyar Kasar Yahudawa

17:56 - September 03, 2013
Lambar Labari: 2584197
Bangaren kasa da kasa, Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Siriya ya bayyana cewar manufar kasar Saudiyya ita ce neman rusa kasar Siriya ta kowace hanya domin kare manufofin kasar Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ganawarsa da gidan talabijin din Al-Manar na kasar Labanon; Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Siriya Faisal Miqdad ya jaddada cewar kasarsa tana cikin shirin kalubalantar duk wani harin wuce gona da iri da makiya zasu kaddamar kanta, tare da kara jaddada cewar duk wani harin wuce gona da iri kan kasar ta Siriya lamari ne da zai wurga zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya cikin mummunar hali.
Har ila yau Faisal Miqdad ya yi tofin Allah tsine kan matsayin gidan sarautar Saudiyya, yana mai bayyana cewar mahukuntan kasar ta Saudiyya sun son ganin sun rusa kasar Siriya ce ta kowace hanya domin kare manufofin kasar Amurka da na haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin gabas ta tsakiya.
Sojojin gwamnatin Siriya sun yi nasarar halaka ‘yan ta’addan kasa da kasa da aka jibge a cikin kasarsu kimanin 90 a cikin sa’o’i 48 da suka gaba a wasu yankunan kasar.
Gidan talabijin din Al-Alam na kasar Iran ya watsa rahoton cewa; duk da barazanar da kasashen yammacin Turai karkashin jagorancin Amurka ke yi na daukan matakin soji kan kasar Siriya: Sojojin gwamnatin Siriya suna ci gaba da samu nasara a yakin da suke yi da ta'addanci, inda suka halaka wasu gungun ‘yan ta’addan kasa da kasa fiye da 40 tare da jikkata wasu da dama daga cikinsu, baya ga kame wasu adadi masu tarin yawa a yankin da ke gefen birnin Damasqas fadar mulkin kasar ta Siriya.
Har ila yau sojojin gwamnatin Siriya sun samu nasarar halaka wasu tarin ‘yan ta’addan da suka haura 40 kuma mafi yawansu ‘yan kungiyar ta’addanci ta Jabhatun-Nusra tare da kame wasu masu yawa a wani kwanton bauna da sojojin suka yi musu a arewacin garin Adrah.
1281920
captcha