IQNA

An zargi shugabannin larabawa da marawa Amurka baya

17:18 - September 04, 2013
Lambar Labari: 2584894
Bangaren kasa da kasa, shugaban Majalisar Dokokin Kasar Siriya ya bayyana cewar sarakunan kasashen Larabawa da suke yankin tekun Pasha suke juya akalar kungiyar hadin kan kasashen Larabawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a ganawarsa da tawagar 'yan kasar Aljeriya da suka ziyarci kasar Siriya domin jaddada goyon bayansu ga gwamnatin Siriya a jiya Lahadi; Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Siriya Muhammad Jihad Al-Lihami ya bayyana cewar yau fiye da shekaru biyu ke nan da gwamnatin Siriya ke fuskantar 'yan ta'addan kasa da kasa da suke samun taimakon gwamnatin Amurka da wasu kasashen yammacin Turai gami da na 'yan koransu na kasashen Larabawa.
Muhammad Jihad ya kara da jaddada wajabcin daukan matakin fuskantar makircin raba kan al'ummar Larabawa musamman a daidai lokacin da sarakunan kasashen Larabawa da suke yankin tekun Pasha suka dauki matakin juya akalar kungiyar hadin kan kasashen Larabawa domin kare munanan manufofin 'yan mulkin mallaka da suke goya musu baya.
Shugaban cibiyar rayar da harkar dimokaradiyya da kare hakkin bil-Adama ta kasar Saudiyya ya bayyana cewar manufar gidan sarautar Saudiyya ta neman kifar da gwamnatin Siriya ita ce kokarin maye gurbinta da ‘yan koran mahukuntan Saudiyya a kasar ta Siriya.

Ali Al-Yami Shugaban cibiyar rayar da harkar dimokaradiyya da kare hakkin bil-Adama ta kasar Saudiyya ya jaddada cewar manufar gidan sarautar Saudiyya na kokarin ganin an kaddamar da harin soji kan kasar Siriya ita ce neman ganin an kifar da gwamnatin Bashar Asad domin maye gurbinta da wata gwamnati da zata kasance mai biyayya ga mahukuntan Saudiyya da nufin raunana kasar Iran, sannan daukan matakin shelanta yaki kan kasar ta Iran.
Al-Yami ya kara da cewar baya ga kokarin gidan sarautar Saudiyya na kunna wutar yaki kan kasar Siriya, haka nan gidan sarautar yana kuma ci gaba da kulla makarkashiyar ruruta wutar rikicin mazhaba a tsakanin al’ummar musulmi duk dai da nufin cimma munanan manufofin da ya sanya a gaba a yankin gabas ta tsakiya.
Ali Al-Yami ya kuma fayyace cewar tabbas kaddamar da duk wani harin wuce gona da iri kan kasar Siriya daga bangaren kasar Amurka da kawayenta na kasashen yammacin Turai lamari ne da zai janyo bullar gagarumin rikici da kashe-kashen rayuka a dukkanin yankin gabas ta tsakiya.

1282639



captcha