IQNA

Amurka za ta shan mummunan kayi matukar dai ta yi gigin kai hari A Syria

17:32 - September 14, 2013
Lambar Labari: 2589448
Bangaren kasa da kasa, rahotannin da suke fitowa daga kasar Siriya na nuni da cewa sojojin kasar sun sami nasarar kwato mafi yawa daga cikin yankunan Ma’alula mai tsoron tarihi da muhimmanci ga mabiya addinin kirista da ‘yan ta’addan kasar suka kame cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.
Kafafen watsa labarai daban-daban sun tabbatar da cewa kimanin kashi 90 cikin dari na garin yana hannun sojojin Siriyan ne bayan wani hari da suka kaddamar a yau din nan a kan ‘yan ta’addan lamarin da ya tilasta musu ranta cikin na kare zuwa ga yankuna da suke kewaye da garin.
A ranar Larabar da ta gabata ce ‘yan ta’addan kasar Siriya na daga kungiyar Jabhatun Nusra da sauransu da suke samun goyon bayan kasashen Saudiyya da Qatar da Turkiyya da kuma wasu kasashen yammaci suka kai hari garin na Ma’alula da ke kimanin kilomita 70 arewa maso gabashin birnin Damaskus inda suka kama mafi yawa daga cikin yankunan garin bugu da kari kan cin zarafin mutanen kasar.
Sojojin Siriyan dai sun sha alwashin fatattakan ‘yan ta’addan daga dukkanin birnin duk kuwa da barazanar da Amurka da kawayenta suke ci gaba da yi na kawo wa kasar hari.
A wani labarin kuma Rahotanni dake fitowa daga Geneva na nuni da cewa akai alamun za;a fahimci juna sakanin kasashen Rasha da Amurka kan tattaunawa batun kasar Syria. Dama dai sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry da na kasar Rasha Sargie Lavrov na a Geneva ne domin tattauna matakan da suka kamata a dauka kan matsalar kasar Syria.
Hakama suna tattaunawa ne domin cire kasar Syria daga jerin kasashe masu Makamai masu Guba a Duniya, kazalika da hana kai harin da kasar Amurka ke yiwa kasar ta Syria, bisa zarginta da amfani da Makamai masu Guba. Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov sun ce tattaunawarsu a kan karbe makamai masu guba daga hannu gwamnatin Syria matakin farko ne na wani babban shiri na kawo karshen rikicin kasar.
A rana ta biyu ta tattaunawarsu a Geneva, hadda wakili na musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan Syria, Lakhdar Brahimi, Mr Kerry ya ce ana samun ci gaba a tattaunawarsu yayin da suke kokarin lalubo matsaya guda.

1286773
captcha