Kamfanindillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, malamai da masana sun yi kira da dauki matakan da suka dace domin kame tare da gurfanar da malamin gwamnatin Qatar Yusuf Qardawi sakamakon haddasa fitina da yake yi tsakanin mabiya addinin muslunci musamman a cikin kasashen larabawa musamman a kasar Syria da Masar.
A wani labarin kuma Ministan sasantawa shiga tsakani na kasar Siriya Ali Haidar ya ja kunnen haramtacciyar kasar Isra’ila da cewa za ta zamanto daya daga cikin wajajen da Siriya za ta kai musu hari matukar dai Amurka ta kawo wa kasar Siriyan hari.
Ministan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar talabijin din Press TV da ke watsa shirye-shiryenta daga nan Tehran inda yayin da yake magana kan ci gaba da barazanar kawo hari kan kasar Siriyan da Amurka take yi inda yace hakkin kasar Siriya na kare kanta zai faro ne daga cikin gida har zuwa wajen kasar. Don haka ya ja kunnen HKI da cewa wajibi ne Siriya ta kai wa haramtacciyar kasar hari matukar Amurka ta kawo mata hari.
Yayin da yake magana kan kasashen da suke ci gaba da kulla makarkashiya ga kasar Siriya da nufin kifar da gwamnatin kasar, Minista Ali Haidar ya zargin shugaban hukumar leken asirin Saudiyya Bandar bin Sultan da hannu dumu-dumu cikin abin da ke faruwa a Siriya da nufin kifar da gwamnatin kasar.
Duk da ci gaba da tattaunawa da ake yi tsakanin Amurka da Rasha don magance rikicin Siriya cikin ruwan sanyi, amma Amurkan taci gaba da barazanar da take yi wa Siriyan lamarin da jami’an kasar suka ce za su yi dukkanin abin da za su iya wajen kare kasar daga duk wani wuce gona da iri na makiya.
1288120