IQNA

Mutane 40 sun rasa rayukansu a wasu jerin hare-haren ta'addanci

15:21 - September 16, 2013
Lambar Labari: 2590601
Bnagaren kasa da kasa, A kalla mutane 40 ne su ka kwanta dama a wasu jerin hare-haren ta’addanci da aka kai a sassa daban-daban na kasar Iraki. Majiyar tsaro ta ce; An kai hare-hare ne da motoci masu makare da bama-bamai a cikin yankuna 11 na tsakiya da kudancin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, hari mafi muni an kai shi ne a cikin gundumar Babil da babban birninta Hullah mai nisan kilo mita 100 a kudu da birnin Bagadaza. Motoci hudu da aka makare da bama-bamai ne su ka tarwatse a cikin birnin tare da kashe mutane 19 da kuma jikkata wasu 36. Wani shaidar ganin ido a garin na Hullah ya fadawa kamfanin Dillancin Labarun Faransa cewa; Da idanunsa ya ga mutanen da su ke cin wuta suna gudu suna neman taimako.”
A Bagadaza kuwa shugaban majalisar birnin ne Riyadh al-addhadh ya tsallake rijiya ta baya a wani harin neman ransa da aka kai da mota mai makare da bama-bamai. Sai dai mutane biyu da su ke tare da shi sun riga mu gidan gaskiya. A gundumar Wasat kuwa mutane 4 ne su ka mutu tare da jikkata wasu 13.
A garin Takrit ‘yan ta’adda sun kashe leburori uku da su ke kokarin shiga motar safa domin zuwa wurin kwadago. Harin na yau ya zo ne kwana daya bayan wasu jerin hare-hare da su ka dauki rayukan mutane 15 da kuma jikkata wasu uku.
1288932












captcha