Bangaren kasa da kasa, Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar kasar Saudiyya tana cikin tsananin fushi sakamakon rashin cimma manufarta ta kifar da gwamnatin Siriya duk kuwa da kokarin da ta yi ba dare da ba rana wajen cimma wannan manufar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen bikin tunawa da shekaru 25 da kafa asibitin Rasulul A’azam a kasar Labanon inda yayi ishara da shan kashin da kasashen da suke adawa da gwamnatin kasar Siriya suke fuskanta a kokarin da suke yi na kifar da gwamnatin kasar wanda ya ce hakan shi ne ya fusata kasar Saudiyya sakamakon gazawar da ta yi na cimma manufarta ta kifar da gwamnati ta hanyar amfani da dukiya da kuma ‘yan ta’addan da take shigo da su Siriya daga kasashe daban-daban na duniya
Shugaban na Hizbullah ya kirayi Saudiyya da sauran masu kafar ungulu ga kokarin da ake yi na magance rikicin Siriya ta hanyar Siriya da su yi amfani da damar da suka samu na tattaunawa kamar yadda ya kirayi kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi da kuma ta kasashen larabawa da su kawo karshen abubuwan da suke kafar ungulu ga magance rikicin kasar Siriyan.
Sayyid Nasrallah ya kara da cewa babu yadda za a yi a bar lamurra su ci gaba da gudana yadda suke a halin yanzu a yankin Gabas ta tsakiya saboda fushin da wata gwamnati ta yi sakamakon kashin da take sha a kasar Siriyan. Sayyid Nasrallah ya ce a halin yanzu dai dukkanin al’ummomin gabas ta tsakiya kama daga musulminsu da kiristocinsu, ‘yan Sunnarsu da ‘yan Shi’ansu suna fuskantar barazana ga rayuwarsu, don haka babu wata hanya guda ta magance wannan matsalar in ba ta hanyar tattaunawa da hanyoyi na siyasa ba.
Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah ya ce ‘yan adawa masu dauke da makami a Siriyan dai sun gagara cimma wani abin a zo a gani a fagen daga yana mai ishara da irin nasarorin da sojojin Siriya da sauran kungiyoyin da suke tare da su suke samu a fagen daga a kasar ta Siriya. Sayyid Nasrallah ya ce sakamakon abin da ke gudana a kas (na irin nasarorin da sojojin Siriya suke samu da kuma kashin da ‘yan ta’adda suke sha), kasashen duniya sun cimma matsayar cewa amfani da karfin soji ba zai magance matsalar Siriyan ba.
1309739