IQNA

Kungiyar Hibullah Ta Yi Allawadai Da Kai Hari Kan Gidan Ayatollah Isa Kasim

20:40 - November 26, 2014
Lambar Labari: 2612331
Bangaren kasa da kasa, kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da harin da jami’an tsaron masarautar Bahrain suka kai kan gidan Ayatollah Isa Kasim.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al-manar cewa, a cikin wani bayani da ta fitar kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakkausar suka dangane da harin da jami’an tsaron masarautar Bahrain suka kai kan gidan babban malamin addini kuma jagoran mabiya mazhabar shi’a a Bahrain Ayatollah Isa Kasim a daren jiya.
A cikin bayanin kungiyar ta Hizbullah ta bayyana wannan lamari da cewa babban abin kunya ne yadda masarautar kasar Bahrain ta fito karara tana fada da al’ummar kasarta, baya ga haka kuma lamarin har ya kai ga mutanen da ake ganin girmansu da darajarsu saboda matsayinsu a cikin al’umma, wanda hakan ya kara tabbatar wa duiniya manufar gwamnatin wannan kasa da cewa it ace murkushe wani bangare mafi girma  akasar saboda dalilai na banbancin mazhaba.
Kungiyar Hizbulla ta kirayi masarautar Bahrain da ta sake yin nazari kan irin wanann babban kure da take tafkawa, domin hakan ba zai taba amfanar da ita ba ko ta wane bangare, maimakon hakan ma irin wannan mataki na rashin lissafi zai kara nisantar da jama’a a daga gare su tare da jawo ma kansu kiyya daga al’ummar kasa.
2612058

Abubuwan Da Ya Shafa: Hezbulla
captcha