
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Time cewa, bisa ga wani bincike da aka gudanar a kasar Birtaniya sunan Muhammad shi ne suna mafi farin jinni a tsakanin al’ummomin kasar Birtaniya a cikin wannan shekara da muke ciki.
Bayanin wannan bincike ya tababtar da cewa daga cikin sunayen larabawa da suka fi samun karbuwa kuwa akwai sunayen Ali, Ibrahim Umar da sauransua tsakanin mutanen da suke rayuwa a kasar musamman dai musulmi da suka zo daga wasu kasashe na larabawa da kuma wadanda ban a larabawa ba.
Haka nan kuma wasu sunayen da aka fi saka wa musamman a tsakanin sunayen mabiya addinin kirista su ne kamar sunan annabi yakub, Nuh da kuma Gabriel da kuma sunayen matan annabi Dawud da kuma tatar annabi Zakariyya wadanda duk suna daga cikin sunaye da suke samu kabuwa a tsakanin al’ummar wannan kasa.
Bincike dai ya tabbatar da cewa akkwai musulmi fiye da dubu 100, kuma adadin yana karuwqa akowace shekara da mutane 5000 bisa la’kari da yadda wasu ke karbar wannan addini, da kuma wasu kasashen larabawa da kuma kasashen musulmi daga wasu nahiyoyin na daban.
2614150