IQNA

Ministocin Sadarwa Na Kasashen Musulmi Sun Shigo Birnin Tehran

7:52 - December 03, 2014
Lambar Labari: 2614554
Bangaren kasa da kasa, mutum 33 daga cikin ministocin harkokin sadarwa na kasashen muslmi na kungiyar OIC sun fara isowa birnin Tehran domin halartaron da za su gudanar a yau.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, tun a jiya ne ministocin harkokin sadarwa na kasashen muslmi na kungiyar sun fara isowa daga cikinsu kuwa har da na kasashen Sudan, Masar, Tunis, Mali, Mauritania, Nigeria, Senegal, Mooco, Saudiyya, Somalia, Pakistan, da kuma UAE.

Ali Aljarwan shi ne shugaban ofishin kula da harkokin sadarwa na hadaddiyar daular larabawa da Sharjah, Abdullah Aljunaidi kuma shi ne mai kula da harkokin sadarwa da yada manufifin kasar ta hanyar kafofin yada labarai, dukkaninsu dai sun iso da nufin halartar wannan taro.

Wannan zaman taro dai zai mayar da hankali kan muhimamn batutuwa da suka shafi kasashen musulmi da kuma yadda ya kamata a mayar da hankali kansu, musamman ma wadanda suke da laka da matsalolin da al'ummar musulmi ke fuskanta a wannan zamani da suka hada bullar wasu abubuwa dab a su cikin addinin musulunci da ake danganta su da musulunci, wadanda ake bata sunansa da su.

Taron dai zai gudana ne a cikin kwanaki biyu tare da halartar ministocin na kasashen musulmi a bangaren harkokin sadarwa tare da tawagogin da suke tare da su, gami da kuma manyan jami'ai na jamhuriyar muslunci.

2614078

Abubuwan Da Ya Shafa: oic
captcha