IQNA

Yaki Da Ayyukan Ta'addaci Na Bukatar Matakai Na Musamman

23:01 - December 05, 2014
Lambar Labari: 2615277
Bangaren kasa da kasa, Isma'il Guna Malangungu wakilain kasar Gabon a kungiyar kasashen musulmi ya bayyana yaki da ayyukan ta'addanci da ake yanzua duniya da cewa yana bukatar daukar matakai na musamman da suka dace.

Kamfanin dillancin labaran iqa ya habarta cewa, a zantawar da ya yi da Isma'il Guna Malangungu wakilain kasar Gabon a kungiyar kasashen musulmi ya bayyana yaki da ayyukan ta'addanci da ake yanzua  duniya da cewa yana bukatar daukar matakai na musamman domin su yi daidai da zamanin da ake ciki.

Isma'il Guna Malangungu ya ci gaba da cewa irin matakan da ake bukata matakai ne da za su akwo sauyi a cikin irin yadda ake nuna wa mutane musulunci, musamman su kansu musulmin wadanda bas u da ilimi, inda wasu akn yi amfani da wannan damar wajen cusa musu munanan akidu da sunan musulunci, wanda kuma hakan a cewarsa yana da matukar hadari.

Akasarin al'ummomin kasashen da ayyukan ta'addanci ke shafa dai  suna ganin cewa babu wani abin a zo a gani da kawancen yaki da ta'addanci ya tabuka ba wajen murkushe 'yan ta'addan a cikin kasashensu, illa dai kawai sojojin wadannan kasashe ne da kuma masu shiga aikin sojin sa kai ne kawai suke yin iyakacin kokarinsu wajen yaki da wadannan 'yan ta'adda.

A bangare guda ma wasu na ganin cewa lamarin ya yi kama da wasan kwaikwayo, idan aka yi la'akari da cewa kasashen da suka kirkiro wadannan 'yan ta'adda kuma suka horar da su musamman ma ita kanta Amurka da wasu kasashen turai, tare da 'yan koransu daga cikin larabawa su ne kuma a lokaci guda a cikin wannan kawance na yaki da wadannan 'yan ta'adda da suka kafa.

Wannan ya sanya wasu masu bin diddigin abubuwan da ke wakana yin imanin cewa, babbar manufar wadannan kasashe ba ita ce yaki da kungiyar 'yan ta'addan ko murkushe ba, domin su ne suka kafa su kuma su ne suka fi kowa saninsu da hanyar da za su iya murkushe su, masu wanann ra'ayin na ganin cewa manufar ita ce rusa kasashen larabawa da na musulmi musamman ma wadanda Amurka da yahudawan sahyuniya suke kallonsu a matsayin barazana a gare su, kuma za a aiwatar da shirin ne ta hanyar yin amfani da wasu daga cikin gwamnatocin musulmin da larabawa da ke kare manufofin Amurka domin aiwatar da wannan shiri.

2614881

Abubuwan Da Ya Shafa: Gabon
captcha