IQNA

Kungiyar Tarayyar Turai Ta Soki Masarautar Bahrain Kan Cin Zarafin 'Yan Adam

23:04 - December 05, 2014
Lambar Labari: 2615278
Bangaren kasa da kasa, kungiyar tarayyar turai ta soki masarautar Bahrain dangane da hakkokin bil adama da ake ketawa a kasar babu ji babu gani da sunan kare masarautar kasar ta mulkin mulukiya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al-alam cewa, kungiyar tarayyar turai ta soki masarautar Bahrain dangane da yadda wannan masarauta ta mulkin mulukiy atake cin zarafin 'yan adam.

Ita ma a nata bangaren kungiyar kare hakkin bil’adama ta afuwa ta duniya ta zargi gwamnatin Bahrain da azabtar da kananan yaran da ta ke tsaro da su, a wani bayani da kungiyar ta fitar ta ambaci cewa a  tun daga shekata ta dubi biyu das ha daya ne ake azabtar da kananan yara masu yawa da ake tsare da su ta hanyar duka.

Rahoton ya ci gaba da cewa wasu daga cikin yaran sun fuskanci barazanar yi musu fyade domin tilasta su yin furuci, mataimakin Shugaban Kungiyar a gabas ta tsakiya da kuma  arewacin Afirka  Said Bu Maduha ya ce; Kame da tsare kananan yara da gwamnatin Bahrain ta ke yi, yana nuni ne da yadda ta ke take hakkokin bil’adama.

Jami’in ya kira yi gwamnatin Bahrain da ta saki dukkanin yaran da shekarunsu su ke kasa da 18 wanda babu wani laifi da su ka aikata, tare da kuma da gudanar da bincike akan  take hakkin bil’adama. Rahoton kungiyar ya ce; Da akwai yaran da adadinsu ya kai daroi da goma da ake tsare da su wadanda kuma shekarunsu su ke a tsakanin sha shida zuwasha takwas, an kuma tsare su a gidan Kurkuku na manyan masu laifi.

2615230

Abubuwan Da Ya Shafa: EU
captcha