IQNA

Tarukar Arba'in Ne Taron Musulmi Mafi Girma A Kasar Iraki

21:52 - December 09, 2014
Lambar Labari: 2617117
Bangaren kasa da kasa, tarukan arba'in da ake gudanarwa a kowace shekara na ci gaba da bunkasa inda a halin yanzu aka bayyana tarukan musamamn na bana da cewa shi ne taro mafi girma na addini a kasar Iraki.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, mutane suna ci gaba da tafiya zuwa birnin karbala na kasar Iraki domin halartar tarukan Arba'in na shahadar Imam Hussain (AS) da za a gudanar hubbarensa da ke birnin.

Mai aiko ma tashar talabijin ta al-alam rahotani daga kasar Iraki ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu dai miliyoin mutane suke tafiya a kasa daga sassa daba-daban na kasar Iraki a kan hanyarsu ta isa birnin na Karbala a hubbaren Imamm Hussain (AS), kamar yadda baki daga kasashen ketare suke isa kasar ta Iraki a iyakokinta na kasa da kuma filayen safkar jiragen sama a biranan kasar.

A nata bangaren rundunar 'yan sanda a kasar ta sanar da kammala daukar dukkanin matakan da suka dace domin bayar da kariya ga masu tarukan na addini na arbain din Imam Hussain (AS), inda yanzu haka jami'an tsaro na hadin gwiwa tsakanin sojoj da 'yan sanda fiye da dubu talatin suke ciki da wajen birnin na Karbala suna gudanar da ayyukansu na tsaro.

2616884

Abubuwan Da Ya Shafa: Arba'in
captcha