IQNA

Ministocin Ilimi Na Kasshen Musulmi Na Shirin Gudanar Da Zama

17:33 - December 14, 2014
Lambar Labari: 2618353
Bangaren kasa da aksa, ministocin ilimi mai zurfi na kasashen musulmi na sirin gudanar da baban zamansua ranakun Alhamis da Juma’a mai zuwa a babban ofishin kungiyar ISESCO da ke birnin Rebat na kasar Moroco.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalato daga shafin sadarwa na aynar gizo na INA cewa, manyan ministocin na ilimi a kasashen musulmi na sirin gudanar da baban zamansu a babban ofishin kungiyar kula da harkokin ilimi da ala’du na kasashen musulmi a birnin Rebat na kasar Moroco tare da halartar Sumayyah Muhammad Abu Kusha daga Suda, kuma tsohowar shugabar kungiyar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wanann taro na daga cikin irin tarukan da kungiyar kan gudanar domin yin bita kan muhimman batutuwa da suka shafi harkokin ilimi mai zurfi a cikin kasashen, tare da duba irin matsalolin da ake fuskanta da kuma sanin hanyoyin magance su, gami da duba irin ci gaban da ake samu da kum bangarorin da ake samun hakan, tare da samo hanyoyin karfafa ci gaban ilmi a cikin wadannan kasashe.
Kungiyar ta jima tana gudanar da tarukanta a kasar Moroco da ma sauran kasashen musolmi mambobi a cikin kungiyar, duk kuwa da cewa akwai kasashe yan kallo wadanda suke cikin kungiyar, kuma sukan dauki nauyin bakunci tarukan wannan kungiyar kula da harkokin ilimi da ala’du na kasashen musulmi.
Kungiyar ta gudanar da taronta na farko bayan kafa a birnin Riyad na Saudiyya a shekara ta 2000, sai karo na biyu a Tripoli na Libya a 2003, sai karo na uku a Kuwait a 2006, sai karo na huhu a Baku Azarbaijan 2008, sai kuma karo na biyar a kualalmpour Malazia 2010, sai kuma a Khartum ta Sudana  2012.
2618218

Abubuwan Da Ya Shafa: Marakesh
captcha