IQNA

Ma’aikatar Harkokin wajen Iran Ta Yi Allawadai Da Garkuwa Da Mutane A Australia

14:58 - December 16, 2014
Lambar Labari: 2620163
Bnagaren kasa da kasa, mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi kakkausar suka da Allawadai da garkuwar da wani dan ta’adda ya yi da mutane a nirnin Sydney na kasar Australia a jiya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ma’aikatar harkokin wajen Iran cewa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Maziyeh Afkham ta yi kakkausar suka da Allawadai da garkuwar da wani dan ta’adda ya yi da mutane a nirnin Sydney na kasar Australia tare da bayyana hakan da cewa yana bata sunan addinin muslunci a idon duniya.
Rahotanni sun ce an kawo karshen garkuwar da mutum dan kasar Australia ya yi da mutane hamsin a birnin Sydney bayan kashe shi har lahira, sakamakon kutsa kai da jami'an tsaron kasar suka yi a cikin wurin tare da bude masa wuta.  
Wasu majiyoyin tsaron kasar ta Australia sun ce mutumin dan asalin kasar Iran ne, wanda yake dauke da akidun wahabiyanci da takfiriyya na kungiyoyin da ke da alaka da alkaida, ya kuma tsare mutanen ne tun jijjifin safiyar yau Litinin a wani dakin shan shayi da Kahwa a birnin Sydney, inda yake dauke da muggan makamai da kuma bakatar tuta mai kama da tutar 'yan ta'addan ISIS masu da'awar jihadin muslunci.

Kungiyoyi da cibiyoyin addinin muslunci fiye da 40 ne  akasar ta Australia suka fitar da bayani a yau na yin Allawadai da wannan aiki, tare da bayyana cewa irin wanann halayya ta saba wa koyarwar addinin muslunci, tare da yin Allawadai da malaman da ke wanke kwakwalen matasa musulmi, tare da tunzura su zuwa ga ayyukan ta'addanci da sunan mulsunci wanda hakan ya saba da abin da yake koyarwa ga mabiyansa.

2618944

Abubuwan Da Ya Shafa: Afkham
captcha