IQNA

Jerin Gwanon Idin Shuhada A Fadin kasar Bahrain

16:40 - December 19, 2014
Lambar Labari: 2622018
Bangaren kasa da kasa, dubban daruruwan al'ummar kasar Bahrain na gdanar da jerin gwanon idin shuhada da suka rasa rayukansu domin neman 'yancinsu a cikin kasarsu a hannun azzaluman mahukunta.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-wifagh cewa, tun a jiya ne al'ummar kasar Bahrain na gdanar da jerin gwanon idin shuhada da suka rasa rayukansu domin neman 'yancinsu a cikin kasarsu sakamakon danninyar da suke fuskanta daga masu mulki.

A bangare guda kuma Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun kwatanta gidajen kason kasar Bahrain da gidajen kason gwamnatin 'yan nazy kasar Jamus karkashin jagorancin shugaban kungiyar a lokacin mulkin jam'iyyar.

A cikin wani bayani da wasu daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama suka fitar jiya daga wata babbar cibiyarsu da ke birnin London na kasar birtaniya sun bayyana irin matakan da mahukunatan kasar Bahrain suke dauke a cikin gidajen kaso wajen azabtar da 'yan adawar siyasa da cewa ya wuce haddi na 'yan adamtaka.

Bayanin ya kara da cewa masarautar Bahrain tana azabtar da 'yan adawar siyasa a gidajen kaso tun daga lokacin fara boren 14 ga Fabrairun 2011, inda aka kashe mutane 150 tare da tsaren wasu ana azabtar da su, da hakan kan kai su ga rasa rayukansu ko wasu bangarorin jikinsu, inda ake yin amfani da duk wani salon a azabtarwa da a kan masu adawa da salon siyasar gidan sarautar kasar.

Kungiyoyin suka ce masarautar Bahrain ta hana kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa su ziyarci mutanen da ake tsare da su a kasar, tare da hana ganawa da mutanen da suka rasa danginsu sakamakon ukubar da masauratar ta Bahrain ta gana musu a gidajen kaso.

2621776

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha