IQNA

Musulmin Nottingham Sun Gudanar Da Zama Kan Tsatsauran Ra’ayi

16:59 - December 28, 2014
Lambar Labari: 2643668
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin musluci a kasar Birtaniya da ke zaune a birnin Nottingham sun gudanar da zama domin tattauna hanyoyin yaki da tsatsauran ra’ayi da ke matasa musulmi zuwa ga ta’addanci.

Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nottingham Post cewa, a daren jiya wasu mabiya addinin musluci a kasar Birtaniya da ke zaune a birnin Nottingham sun gudanar da zama domin tattauna hanyoyin yaki da tsatsauran ra’ayi da ke matasa musulmi zuwa ga ta’addancia  cikin kasashen musulmi da na turai da wasu kasashen duniya.
A wani bayanin na daban kuma wata babbar cibiyar musulmi ta dauki nauyin shirya wannan jin ra’ayin jama’a da kuma fitar da wannan sakamako da ke cewa cewa adadin mutanen ad suke karbar addinin muslunci a kasar Birtaniya a cikin shekaru goma da suka gabata ya nunka har sau biyu.
Wasu da dama daga cikin fiye da kashi sittin wadannan mutane ne dai sun nuna cewa sun karbi muslunci ne sakamakon binciken da suke gudanarwa wanda haka ne yaba su damar daukar kudirin karbaer musulunci, sakamakon abin da suka gano a cikinsa na koyarwa ta hakika wadda mutum dan addam ke samun kamala da ita a cikin rayuwarsa ta duniya.
Wannan ya zo ne duk kuwa da cewa ana ta maganar ayyukan ta’addanci da ke bata sunan mus;nci sakamakon abin da ak shirya na bata sunan addinin ta hanyar yin amfani da wasu gurbatattun musulmin kuma bata gari, amma bayan bincike sun gane cewa addinin musulunci na zaman lafiya ba kamar yadda ‘yan ta’adda ke nunawa ba, ko kuma makiya addini kamar dai yadda hakan bai buya ga kowa a duniya ba.
2642466

Abubuwan Da Ya Shafa: birtaniya
captcha