Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Local Berkshire cewa, daga cikin manyan asibiton kasar Birtaniya a garin Slogh ta shirya gina wani wurin alwalla domin kyatata ma musulmi marassa lafiya masu samun zuwa wurin.
Wata cibiyar musulmi ta dauki nauyin shirya wannan jin ra’ayin jama’a da kuma fitar da wannan sakamako da ke cewa cewa adadin mutanen ad suke karbar addinin muslunci a kasar Birtaniya a cikin shekaru goma da suka gabata ya nunka har sau biyu kamar yadda aka bayyana.
Fiye da kashi sittin wadannan mutane ne dai sun nuna cewa sun karbi muslunci ne sakamakon binciken da suke gudanarwa wanda haka ne yaba su damar daukar kudirin karbaer musulunci, sakamakon abin da suka gano a cikinsa na koyarwa ta hakika wadda mutum dan addam ke samun kamala da ita a cikin rayuwarsa.
Hakan ya zo ne duk kuwa da cewa ana ta maganar ayyukan bata gari da ke bata sunan mus;nci sakamakon abin da ak shirya na bata sunan addinin ta hanyar yin amfani da wasu gurbatattun musulmin kuma bata gari.
Amma bayan bincike sun gane cewa addinin musulunci na zaman lafiya ba kamar yadda ‘yan ta’adda ke nunawa ba, ko kuma makiya addini kamar dai yadda hakan bai buya ga kowa a duniya ba bisa bincike.
2646933