Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a zantarwa da yay i da Abdulali Muhammad sadighi wanda ya wakilci kasar Iraki a gasar karatun kur’ani ta kasa da kasa ya bayyana cewa gudanar da irin gasa yana da matukar muhimmanci wajen kara hada kan al’ummar musulmi na duniya baki daya kamar dai yadda yake faruwa.
Ita dai wannan na daga cikin gasar da ake gudanarwa a matsayi na kasa da kasa a jamhuriyar musulunci da ke samun halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya, wanda a wannan karon ma an samu halartar wasu daga kasashe daban-daban da suka hada da nahiyar turai baki daya.
Yana daya daga cikin abubuwan da wannan gasa ta kebanta da su dai su ne bayar da muhimmanci ga kyautata karatu domin ya zama matashiya ga sauran makaranta, tare da samar da salon a karatu da harda a lokacin gasa, wanda shi ne irinsa bna farko, duk da nufin karfafa harkokin karatu da hardar kur’ani mai tsarki a tsakanin matasa na kasashen musulmin duniya.
Duk da cewa gasar dai ta banbanta dasauran, musamman ma ganin cewa dukkanin mahalrtanta daliban jami’oi ne a cikin kasashn musulmi na duniya, daga karshe kuma ana bayar da kyautuka na musamman ne ga wadanda suka fi nuna kwazo, sai kuma kyautuka na baki daya ga duk wanda ya halarta.
2670564