
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo news press cewa, a jiya masallacin birnin Paris na kasar Faransa ya fitar da bayani a loacin tarukan maulidin manzon Allah, inda bayanin yay i nuni da cewa dole ne musulmi su yi amfani da wannan domin haduwa domin tunawa shugabansu jagoransu.
Bayanin ya ci gaba da cewa abin da yake a gaban musulmi a halin yanzu shi ne, su tabbatar wa duniya da cewa tunanin da ake yi dangane da addinin muslunci da musulmi bah aka ba ne, domin kuwa shi musulunci addin ne na zaman lafiya da fahimtar jun ad akuma sulhu.
Taron ya hada da karatun kur’ani mai tsarki, da kuma wakokin yabon manzo domin tuwa da wadannan ranaku masu albarka, kamar dai yadda bayanin ya nuni.
2683065