IQNA

Daya Daga Cikin Wadanda Aka Kashe Harin Kasar Faransa Musulmi Ne

12:43 - January 12, 2015
Lambar Labari: 2699756
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin jami’an tsaron da aka kashe a Faransa mai suna Ahmad Murabit musulmi ne kamar dai yadda bayanai suka tabbatar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Telegraph cewa Ahmad Morabit dan sandan da ya rasa a harin da aka kai kan jaridar Charlie Hebdo musulmi ne.
Kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa ya habarta cewa, jim kanan bayan harin da wasu 'yan bindiga suka kai wa gidan jaridar Charlie hebdo ta birnin Paris a jiya laraba, Al'umma sun yi cuncurundo a dandalin Republicain domin nuna rashin jin dadinsu da abin da ya faru.
Kimanin karfe sha daya na safiyar laraba ,wasu mutane uku dauke da makamai suka kai  farmaki gidan jaridar barkoncin nan ta Charlie hebdo dake birnin Paris inda suka kashe Mutane sha biyu tare da jikkata wasu goma na daban.
Shi dai wannan gidan jarida shi ne ya zana  hoton batanci ga fiyayyen halitta Manzon a..tsira da amincin a..su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka,lamarin da ya sanya Jaridar da ma Gwamnatin Faransa suka sha suka daga kasashen musulmi.
‘Yan sandar birnin Paris sun ce sun gano wadanda ake tuhumar da kai wannan hari, inda tuni dai daya daga cikinsu mai shekaru sha takawas a duniya ya meka kansa ga hukumar 'yan sandar, kuma yanzu haka hukumomin 'yan sandar ta ce ta na farauta sauren mutanan biyu.
Kasashen duniya na ci gaba da yin Allawadai da harin da 'yan bindigar suka kai a gidan mujallar nan ta Charlie Hebdo dake kasar ta Faransa, tare da bayyana irin wadannan ayyuka da cewa na dabbanci ne, yayin da wasu suke yin Allawadai da hakan, sun kuma dora alhakin abin da yake faruwa a kan mahukuntan kasar da kuma jaridar, sakamakon abin da take yin a cin zarafi.
2692007

Abubuwan Da Ya Shafa: Fransce
captcha