IQNA

A Yau Ne Gudanar da Shari’ar Jagoran Adawa A Bahrain Sheikh Ali Salman

17:03 - January 28, 2015
Lambar Labari: 2774755
Bangaren kasa da kasa, a yau ne ake gudanar da shari’ar jagoran jam’iyyar Alwifaq babbar jamiyyar adawa a kasar Bahrain Sheikh Ali Salman a gaban kuliya domin hukunta shi kan dalilai na siyasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jam’iyyar Alwifaq cewa, mahukuntan Bahrain a yau ne suke gudanar da shari’ar jagoran jam’iyyar Alwifaq  babbar jamiyyar adawa  a kasar  Sheikh Ali Salman a gaban kuliya tun bayan da suka kame shia  kwanakin baya.
Wannan shari’a dai tana zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar kasar suke ci gaba da yin bore da kuma neman a saki Sheikh Salman wanda ake tsare da shi bisa dalilai na siyasa, duk kuwa da matakan da mahukuntan suke dauka na yin amfani da karfi domin murkushe masu zanga-zangar.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun kwatanta gidajen kason kasar Bahrain da gidajen kason gwamnatin 'yan nazy a kasar Jamus karkashin jagorancin shugaban kungiyar a wancan lokaci.
A cikin wani bayani da wasu daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama suka fitar jiya daga wata babbar cibiyarsu da ke birnin London na kasar Birtaniya, sun bayyana irin matakan da mahukunatan kasar Bahrain suke dauke a cikin gidajen kaso wajen azabtar da 'yan adawar siyasa da cewa ya wuce haddi na 'yan adamtaka.
Bayanin ya kara da cewa masarautar Bahrain tana azabtar da 'yan adawar siyasa a gidajen kaso da hakan kan kai su ga rasa rayukansu ko wasu bangarorin jikinsu, inda ake yin amfani da duk wani salon a azabtarwa da a kan masu adawa da salon siyasar gidan sarautar kasar.
Kungiyoyin suka ce masarautar Bahrain ta hana kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa su ziyarci mutanen da ake tsare da su a kasar, tare da hana ganawa da mutanen da suka rasa danginsu sakamakon ukubar da masauratar ta Bahrain ta gana musu a gidajen kaso.
2772380

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha