IQNA

An Bude Masalalcin Mata Na Farko A Kasar Amurka

18:42 - February 01, 2015
Lambar Labari: 2795035
Bangaren kasa da kasa, an bude wani masalalci na mata a birnin Los Angeles na kasar Amurka domin gudanar da sallolin jama’a.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na La Times cewa, a cikin wannan mako ne aka bude wani masalalci na mata yan kasashen China, Chily da kuma India a kasar Amurka domin gudanar da salloli.
A cikin makon da ya gabata shugaban kasar Amurka ya yi kakkausar suka da yin Allawadai da da abin da ya kira nuna kiyayya ga yahudawa sai kuma cin zarafin da ake yi wa mabiya addinin muslunci a cikin wasu kasashen turai.
A lokacin da yake gabatar da jawabin nasa na jiya a gaban majalisar dokokin kasar ta Amurka, bayanin ya mayar da hankali kana bin ake kira tozarta yahudawa da kuma nuna musu kyama, duk kuwa da cewa ya yi kokari ya nuna damuwarsa kana bin da ake yi wa mabiya addinin muslunci a cikin wasu kasashen ymmacin turai na cin mutunci.
Shugaban na Amurka y ace babu wani dalili da wani bangare zai tsani wani bangare, dmin kuwa a cewarsa a halin yanzu dukkanin duniya ta zama bu guda uma ana bukatar hadin kai tsakanin dukkanin al’ummomi domin tunkarar barazanar ta’addanci wadda ba ta bar kowa ba kamar dai yaddad ya fada a cikin wannan jawabi nasa.
Haka nan kuma ya bukaci da a daina  azuzuta wutar riki ta hanyar yin bayanai masu kushi da kuma sosa zuciya, matukar ana bukatar zaman lafiya a tsakanin dukkanin al’ummu.
2793870

Abubuwan Da Ya Shafa: America
captcha