IQNA

An Gudanar da Tarukan Ranar Hijab Ta Duniya Baki Daya

17:03 - February 03, 2015
Lambar Labari: 2804015
Bangaren kasa da kasa, dubban mata ne musulmi da ma wadanda ba musulmi ba suka samu nasarar gudanar da taruka na ranar Hijab a kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa a ranar Hijab ta duniya wato World Hijab Day an gudanar da taruka da saka bayanai a kafofin sadarwa na yanar gizo na facebook da sauransu.
Wata daya daga cikin wadanda suka shiga cikin shirin ta bayyana cewa hakika ta ji dadin hakan, tare da bayyana cewa hijabi ya zama babban abin alfahari da ado da kawa a wajenta, ta yadda ya zama shi ne abin da take sakawa matukar dai tana son ta samu natsuwa.
Haka nan ma wasu daga cikin wadanda suka shiga cikin shirin daga kasashen duniya, da suka hada har ma da wasu matan wadanda ba musulmi ba, da suka taya yan uwansu mata musulmi murnar wannan rana, sun nuan yadda lamarin yay i musu tasiri matuka, domin kuwa hijabi ba lamari ne da ya kebanci muslmi ba kawai, hatta ma wadanda ba musulmi sun amfana da hijabi.
Kamar yadda aya zoa  cikin wasu addinai da suka gabaci muslunci hijabi sutura ce ta dukkanin addinai da suka safka daga sama, wanann ta fuskar addini kenan kenan, baya ga haka kuma a hankalce mace tafi samu natsuwa  aloacin da ta rufe jikinta a tsakanin al’umma, kamar yadda mata da dama da ba musulmi ba suka yi nuni da hakan.
A kasashe dari da sha shida ne mata musulmi suka gudanar da taruka na raya hijabin muslunci, inda kuma aka sanya ranar 1 ga watan Fabrairu na kowace shekara a matsayin ranar Hijabi ta duniya. A wasu kasashen an samu halartar mata da ba musulmi ba a tarukan da mata musulmi suka shirya.
2801690

Abubuwan Da Ya Shafa: Hijab
captcha