IQNA

Kungiyar PEGIDA Mai Kiayya Da Musulunci Na Shirin Gudanar Da Jerin Gwano A England

19:20 - February 15, 2015
Lambar Labari: 2855083
Bangaren kasa da kasa, a karon farko kungiyar nan mai tsananin gaba da kiayya addinin muslunci ta PEGIDA na gudanar da jerin gwano a cikin watan Maris mai kamawa a kasar Birtaniya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar faransa cewa, ya nakalto daga shafukan yanar gizo cewa kungiyar ta masu tsssaurin ra’ayin kiyayya da muslunci ta PEGIDA na shirin gudanar da wannan zanga-zanga ne bayan da kimanin mutane 600 suka ce za su shiga jerin gwanon.
Ita dai wanann zanga-zanga za su gudanar da ita ne kianin watanni biyu bayan gudanar da zabukan yan majalisar dokokin kasar ta Birtaniya, kuma bisa taken cewa yankin turai na turawa ne kawai masu kiyayya da muslunci tsalla.
A cikin yan makonnin da suka gabata wannan kungiya ta gudanar da irin wannan gangami a gabacin kasar Jamus tare da halartar yayan kungiyar na jamus da ma wasu daga cikin kasashen turai wadanda suke da ra’ayi da kuma mahanga guda kan addinin muslunci.
Duk hankoron wannan kungiya na bata sunan muslunci, amma kuma a lokaci ana samun ci gaba ta fuskar raguwar wadanda suke halartar tarukan kungiyar a cikin kasashen turai.
2853852

Abubuwan Da Ya Shafa: PEGIDA
captcha