
Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Manarah cewa, kamfanin kasar Fillad na ALE ya sanar a jiya cewa zai fara watsa shirin kur'ani ta hanyar radio wanda za a kasa 60 kuma wane shiri mintuan 30 daidai.
Babbar manufar gudanar da wannan shiri dai ita ce kara fahimtar da mutane a kasar ta Filland dangane da addinin muslunci, ta yadda ahakan zai taimaka matuka wajen kara samun zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai, maimakon tsangwamar mabiya muslunci ba tare da sanin hakikanin addininsu ba.
Wani malamain jami'a mai suna professor Jaco Haymin Antila ya bayyana cewa, wannan shiri yana da matukar muhimmanci, kuma yana daga cikin wadanda suka kara karfafawa matuka domin ganin an gudanar das hi, domin kuwa shi ne ya tarjama kur'ani mai tsarkia cikin harshen larabaci zuwa harshen kasar.
Ya kara da cewa rashin sani shi ne babban tushen dukkanin matsaloli, domin da mutane sun san kur'ani da abin da yake koyar da dan adam da ba su tsani mabiya addinin muslunci ba, amma a halin yanzu an dauki hanyar yin gyara.
Musulmin kasar Filland dai sun kai kimanin dubu 60, kuma akasarinsu 'yan gudun hijira ne daga kasashen Iraki da kuma Somalia.