Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi cewa, a lokacin ganawar Ahmad Tayyib da kuma Sa’ad Hariri shugaban jam’iyyar Al-Mostaqhbal ta kasar Lebanon ya bayyana wajabcin hada kai domin shiga kafar wando daya da ‘yan ta’addan da suke barazana ga zamana lafiyar al’ummomin yanin gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.
Jami’ar ta kirkiro wata cibiya ta yanar gizo a kokarin da take yin a fada da tsaurin ra’ayi na addini da ya fara zama karfen kafa ga kasashen duniya musamman kasashen musulmi, inda ake yaudarar yara matasa musulmi da sunan addini wajen aikata ayyukan ta’addanci a duniya, wanda hakan ke bata sunan wannan addinin mai tsarki.
Yayin da yake sanar da hakan daya daga cikin manyan jami’an Jami’ar ta Azhar ya ce a halin yanzu dai bisa la’akari da irin yadda masu tsaurin ra’ayin suke amfani da hanyoyin sadaukar na zamani wajen yada akidunsu don haka ya zama wajibi a kirkiro hanyoyi na zamani wajen fada da wannan shiri na su.
Jami’in ya kara da cewa ta hanyar wannan sabuwar cibiyar za a sami damar wayar da kan mutane kan hakikanin koyarwar Musulunci da kuma rashin ingancin abubuwan da masu tsaurin ra’ayin suke yadawa da kuma hanyoyin da suke bi wajen janyo hankulan mutane zuwa gare su.
2953163