
Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-riyadh cewa, Sa’ud Bin Naif bin Abdul azizi gwamnan lradin gabacin kasar ya samu halartar taron da aka yi.
Abdullah Bin Furain Al-bahlal shi ne shugaban cibiyar gudanar da ayyukan alkhari a yankin, ya bayyana cewa za a bude wannan babbar cibiya ne Al-jubail tare da taimakon gwamnan lardin na gabacin kasar, wanda a cewarsa ya bayar da dukkanin taimakon da ya kamata.
Ita ma a nata bangaren cibiyar tasa ta shiga cikin aikin gadan-gadan domin tabbatar da cewa an kai cimma nasa a cikin kankanin lokaci, ta yadda malaman za su fara samun horron da ya dace domin su fara koyar da mata da kuna yara a yankin.
Wanann shiri dai ya samu karbuwa daga al’ummar yankin wadanda mabiya mazhabar shi’a ne, wadanda suke fuskantar matsaloli na mayar da saniyar ware a cikin lamarran tafiyar da kasa wadda ke bin tsarin mulukiya.