IQNA

Alkawalin Shugaban Najeriya Na Kawo Karshen Boko Haram Cikin Kwanaki 30

23:12 - March 21, 2015
Lambar Labari: 3021906
Bangaren kasa da kasa, a kwanakin baya ne shugaban Najeriya ya yi alakawalin cewa za a kawo karshen kungiyar yan ta'adda ta Boko Haram a cikin kwanaki 30 a Najeriya baki daya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na BBC cewa, a jiya Juma'a a wata zantawa da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana cewa, alkawalin day a dauka yana ganin haske dangane da lamarin, dangane da nasarorin da ake samu wajen yaki da Boko Haram a kasarsa.

Dangane da zaben da za a gudanar kuwa, shugaban Nigeriya ya yi alkawarin ganin an gudanar da ingantaccen zabe cikin zaman lafiya a watan Fabrairu mai kamawa tare da rantsar da duk dan takarar da ya lashe zaben shugabancin kasar a wata Mayu kamar yadda doka ta shimfida.
Wannan furuci na shugaban Nigeriya Goodluck Ebele Jonathan ya zo ne a ganawarsa da wasu jami'an kasashen ketare da suka ziyarci kasar Nigeriya a jiya Lahadi; kuma wannan alkawari da shugaban Nigeriya ya yi ya zo ne a daidai lokacin da wasu mutane ciki har da mai ba shi shawara kan tsaron kasa suke kira kan dage zabuka da aka shirya gudanarwa a kasar ta Nigeriya ciki har da na shugaban kasa a watan Fabrairu mai kamawa.
Bukatar neman dage lokacin gudanar da zabuka a Nigeriya da suka gabatar ta fuskanci mai da martani daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar  da kuma babbar jam’iyyar adawa ta kasar.
3013791

Abubuwan Da Ya Shafa: Jonathan
captcha