IQNA

Ba Za Mu Amince Da Kai Harin Saudiyya A Kasar Yemen Ba

20:33 - March 30, 2015
Lambar Labari: 3062616
Bangaren kasa da kasa, Agha Sayyid Muhammad Redha wakili a majalisar hadin kan a’ummar musulmi a kasar Pakistan ya bayyana cewa ba za su taba amincewa da matakin da kasar ta dauka na bin sahun Saudiyya wajen kashe al’ummar kasar Yeman ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Agha Sayyid Muhammad Redha wakili a majalisar hadin kan a’ummar musulmi a kasar Pakistan daga yankin Balochestan, a zantawarsa da manema labarai ya sheda cewa, ko alama ba za su taba amincewa da matakin da kasar ta dauka na bin sahun Saudiyya wajen kashe al’ummar kasar Yeman ba wanda ya bayyana da cewa zalunci ne.
Shi ma a nasa bangaren shugaban asha ya kirayi shugabannin kasashen larabawa musamman Saudiyya da kuma kasashen ad suka bi sahunta wajen kaddamar da hari kan kasar Yemen da suna yaki da 'yan kungyar husi  da su sake yin nazari kana bin da suke yi. 

Shugaba ya bayyana hakan ne a cikin sakon da ya aike zuwa ga taron kasashen larabawa da aka gudanar wanda babban jami'in kasar kan harkokin larabawa da yankin gabas ta tsakiya ya karanta a gaban, ya kuma jadda yau a zantawarsa da wasu daga cikin ministocin harkokin wajen kasashen larabawa.

Bayanin na shugaban ga shugabannin kasashen larabawa ya kiraye da su fifita hanyoyin zaunar da bangarorin rikici a kasar Yemen kan teburin tattaunawa, maimakon kira zuwa ga hada rundunar sojojin kasashen larabawa domin yin lugudan wuta kan al’ummar Yemen da sunan yaki da wata kungiya guda a kasar.

Rahotanni daga kasar ta Yemen sun tabbatar da cewa jiragen yakin masarautar Saudiyya da ke rike da madafun iko a Saudiyya sun ludan wuta a kan babban tashar da ke samar da wutar lantarki ga jahar sada da ke arewacin kasar Yemen, harin da ya lalata wannan tashar wutar lantarki baki daya, kamar yadda kuma wasu hare-haren suka nufi babbar tashar samar da iskar gas ta jahar, inda ita ma suka lalalta baki daya.

3059574

Abubuwan Da Ya Shafa: PKSTN
captcha