Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na oic-oci.org cewa, Iyad Amin Madani mai Magana da yawun kungiyar ya bayyana cewa, kungiyar na shirin gudanar da wani taro domin nuna goyon baya al’ummar palastinu da kuma kin amincewa da ci gaba da gina matsugunnan yahudawa a cikin sauran yankunansu da ake mamayewa.
Ya sanar da hakan ne a taron da shugabannin kasashen larabawa suka gudanar a yankin Sharm Shikh na kasar, inda suka kdirci kafa wata rnduna ta bai daya ta kasashen larabnawa domin tabbatar da abin da suke kira tsaron larabawa, duk kwa da cewa wasu daga cikin kasashen sun yi watsi da wannan batu, inda suke kallon cewa kawai wata kasa c eke son ta yi amfani da su, kamar yadda a halin yanzu take yin amfani da wasu da ta dauka haya daga cikinsu.
A taron dai batun Palastinu bai zama daya daga cikin abubuwa masu muhimamnci ba, domin kuwa batun yeman ne kawaui aka tatatuna da kuma yadda za a ci gaba da kai mata hari ta sama da kasa da sunan yunkurin dawo da halastacciyar gwamnati a kasar, wanda kuma yan amashin shata daga cikin wadannan kasashe sun amince da hakan.
Salah Bardawil daya daga cikin jagororin Hamas ya bayyana cewa, taron na Sharm Sheikh bas hi da banbanci da sauran wadanda suka rigaye shi, domin kwa batun killace Gaza da yahudawa ke yi bai dfa muhimmanci a taron sai da I wasu batutuwa na daban da suka shafi maslahar wasu daga cikin kasashne da ke taron kawai.