Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Iraq99.com cewa, a jiya daruruwan jama’ar kasar Saudiyya ne suka gudanar da zanga-zanga a garin Awamiyah da ke gabashin kasar don nuna rashin amincewarsu da hukumcin kisan da wata kotu ta yanke wa fitaccen malamin Shi’a na kasar Sheikh Nimr Bakir al-Nimr da kuma wasu mutane bakwai da su ma aka daure su sakamakon zanga-zangar da suka yi a baya.
Rahotanni daga Saudiyyan sun ce mutanen sun fito ne bayan sallar Juma’a a yau din nan don nuna rashin amincewarsu da wannan hukumci da suka bayyana shi da cewa hukumci ne na zalunci da nuna wariya da mahukuntan Saudiyyan suka yanke wa wannan malamin da kuma sauran mutane din da aka kama su sakamakon fitowa zanga-zanga.
A ranar Talatar da ta gabata ce wata kotun Saudiyya ta yanke wa wasu mutane biyu daga cikin takwas din hukumcin kisa saboda samunsu da laifin tada hankalin mutane a yankunan ‘yan Shi’a tun shekaru ukun da suka gabata.
Kungiyoyin kare hakkokin bil’adama dai sun yi Allah wadai da wannan hukumcin suna masu cewa mutanen da aka yanke wa hukumcin kisan, suna kananan yara ne a lokacin da aka kama su. ‘Yan Shi’an kasar Saudiyyan dai suna fuskantar takuri da nuna wariya daga wajen gwamnatin Saudiyyan.
Jamhuriyar Musulunci ta nuna damuwarta ainun dangane da hukumcin kisan da wata kotun kasar Saudiyya ta yanke wa fitaccen malamin ‘yan Shi’a na kasar Ayatullah Sheikh Nimr Baqir al-Nimr tana mai cewa zartar da hukumcin na iya fusata al’ummar musulmi.
3303907