IQNA

Amnesty International Ta Bukaci Gidan Sarautar Bahrain Su Sakin Sheikh Salman

23:43 - June 16, 2015
Lambar Labari: 3315294
Bangaren kasa da kasa, kungiyar Amnesty International ta bukaci a saki Shekh salman sakataren jam’iyyar Alwifagh a Bahrai ba tare da wani bata lokaci ba.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwifagh cewa, Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta bukaci hanzarta sakin jagoran ‘yan adawar kasar Bahrain Sheikh Ali Salman.

A bayanin da kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta fitar a jiya Litinin  yana dauke da sanarwar cewa; Mahukuntan gidan sarautar Bahrain suna tsare da Sheikh Ali Salman babban sakataren jam’iyyar Al-Wefaq kuma jagoran ‘yan adawar kasar ne saboda furta albarkacin bakinsa ta hanyar lumana, don haka tana kira ga mahukuntan Bahrain da su hanzarta sakinsa ba tare da gindaya wani sharadi ba ko bata lokaci..

Har ila yau kungiyar ta Amnesty International ta bukaci gidan sarautar Bahrain da ta mutunta hakkin furta albarkacin baki da duk wani yunkurin ‘yan adawa ta lumana tare da kawo karshen dokokin da suka hana kafa kungiyoyi da jam’iyyun siyasa a kasar.

Tun a ranar asirin da takwas ga watan disamban shekarar da ta gabata mahukuntan Bahrain suke tsare da Sheikh Ali Salman saboda furta rashin amincewarsa ga munanan matakan da ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ke dauka kan ‘yan adawan Bahrain.

3314900

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha