Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa, kotun birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar da take shari’ar hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi da wasu mukarrabansa na kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood.
A yayin zamanta na yau Asabar ta yanke hukuncin kisa kan hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi kan laifin wurga tsaron kasar ta Masar cikin hatsari ta hanyar sanar da kasar atar bayanan sirrin kasa da kuma gudu daga gidan kurkuku a shekara ta 2011.
Har ila yau kotun ta yanke hukunci kisa kan mukarraban hambararren shugaban su dari kan samunsu da laifin fasa gidan kurkuku a lokacin tarzomar juyin juya halin da aka a kasar da ta kai ga kifar da gwamnatin Husni Mubarak a shekarar.
A halin yanzu haka dai alkalin kotun zai mika takardun hukuncin da ya yanke zuwa gaban babban malamin gwamnatin kasar mai bada fatawar addini domin yin nazari kan hukuncin domin bayyana mahangarsa kafin hukuncin ta zame karbabbiya. Tuni dai Muhammad Morsi da ke sakaye a cikin keji a kotun ya daga murya yana bayyana rashin amincewar da shari’a tare da yin watsi da hukuncin.
Kungiyar kare hakin bil adama ta duniya ta ce hukuncin kisan da kotun Masar ta yankewa Hanbareren shugaban Muhamad Morsi ba sabawa dokokin kasa da kasa. Jim kadan bayan yanke hukuncin kisa kan hambararen shugaban kasar Masar Mohamad Mursi, kungiyar kare hakin bil-adama ta duniya ta fitar da sanarwa inda ta ce wannan hukunci ya sabawa dokokin kasa da kasa sannan ta bukaci gwamnatin ta Masar da ta saki hanbararen shugaban kasar ko kuma a sake yi masa shara’a ta adalci a wata kotu ta fararen hula.