Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Almayadeen cewa, yahudawan sun kai farmaki kan majami’ar tare da kone ta da wuta kurmus, tare da lalata dukkanin abin da ke cikinta.
Wannan dai ba shi ne karon farko da wadannan yahudawa suke gudanar da irin wadannan ayyuka na wuce gina iri ba, domin kuwa a lokutan bayan sun kai irin wannan hari kuma sun kona kaddarorin mabiya addinin kirsita, kamar yadda suke yi kan na musulmi.
A wani labarain kuma rahotanni sun bayyana cewar an fuskanci matsala da rashin nasara cikin wani gwajin wata sabuwar garkuwar makamai masu linzami na hadin gwiwa tsakanin Amurka da yahudawa a kokarin da suke yi na tabbatar da tsaron Isra’ila daga hare-haren da za ta iya fuskanta daga makamai masu linzami masu cin dogon zango.
Maaikatar tsaron yahudawan ta sanar da cewa sun gwada wata na’urar kakkabo makamai masu linzami masu cin dogon zango sai dai ma’aikatar ba ta yi karin bayani kan abin da ya gudana ba, inda wasu kafafen watsa labaran cikin gida suka ce an dakatar da gwajin ne jim kadan bayan fara shi.
Wannan dai ba shi ne karon farko da irin wadannan na’urori na garkuwar suke fuskantar matsala ba hatta a lokacin yaki inda a mafi yawan lokuta sun gagara kakkabo makamai masu linzamin da aka harbor.
3315856