Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo an Al-alam cewa, Ahamd Tayyib babban wanda kuma shi ne malamin cibiyar Azhar da ke kasar masar, a wannan karo ya zare takobinsa da nufin yaki da yaduwar akidar mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) da aka fi sani da shi’a.
Ya cea wannan wata na Ramadan zai mayar da hankali ne tafsirin kur’ani da yake yi kan falalar sahabbai, da kuma bayyana matsayin yan shi’a da suke fadar abubuwan da sahabbai suka aikata, da kuma bayyana hakan a matsayin akidarsu.
Wani abu da ya baiwa masu hankali ammaki shi ne yadda malamin ya dauki wannan matsaya adaidai wanann lokaci da al’ummar musulmi suke bukatar hadin kai, musamman ganin yadda irin babban kalu bale da ake a gabansu, wanda kuma malamai ne ya kamata su fadakar da musulmi su kara kusanto da su ga juna.
Sau da dama malamin yak an dauki matakai masu kama da wannan wajen sukar tafarkin iyalan gidan manzon Allah, inda yake cewa baa i taba yarda da yan shia ba har sai sun ce babu abin bauta da gaskiya sai Allah kuma Muhammad amnzonsa ne, su daina hada hakan da cewa Ali waliyin Allah ne, kuma su daina dangane da maganganun da y ace na batunci ne ga Aisha uwar muminai.
Y ace yana kirana matasa da su yi hattara da masu jan hankulansu zuwa ga mazhabar shi’a da sunan suna yada son iyaan gidan manzo, wanda y ace ta wanann hanyar ne ake rudar masu rauni da kuma jahilai sais u fada cikin bin shi’a.
316167