Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NLTimes cewa, wata kotu a Autria ta ce dole ne a hukunta Geert Wilders dan majalisa mai cin zarafin addinin Musulunci.K
otun daukaka kara ta bada umurnin a gurfanar da Geert Wilders bisa zargin cewa maganganun batunci ga Musulmi da addininsu da ya yi a kafafen watsa labarai suna tunzura mutane don su nuna kiyayya da bambamci ga wasu jama'a.
Masu shigar da kara sun sami kiraye-kiraye masu yawa na bukatar a duganar da bincike saboda wani fim da Wilders ya shirya wanda ya kira "Fitna" da kuma maganganun ya yi a jaridu, wadanda suka hada da inda ya kwatanta Al'kur'ani mai girma da Mein Kampf littafin da Hitler ya rubuta, ya kwatanta addinin Musulunci da akidar Nazi.
Wannan aiki na dan majalisar kasar Holland din ya fuskanci maida martani mai tsanani daga al'ummar Musulmi.
3336616