Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwast cewa, sheikh Maisam Salman cewa dole ne akawo karshen kafirta mabiya mazhabar shi’a da wasu ke yi tare da goyon bayan mahukuntan kasar.
Hakan nan kuma yay i Allawadai da rusa masallatan yan shi’a da ake babu gaira babu sabar sai dai saboda dalilai na siyasa, tare da kokarin mayar da su saniyar ware, alhali su ne masu rnjaye a kasar fiye da kowa.
Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta bukaci hanzarta sakin jagoran ‘yan adawar kasar Bahrain Sheikh Ali Salman.
A bayanin da kungiyar kare hakkin bil-Adama ta fitar a jiya Lahadi yana dauke da sanarwar cewa; Mahukuntan gidan sarautar Bahrain suna tsare da Sheikh Ali Salman babban sakataren jam’iyyar ‘yan adawar kasar ne saboda furta albarkacin bakinsa ta hanyar lumana, don haka tana kira ga mahukuntan Bahrain da su hanzarta sakinsa ba tare da gindaya wani sharadi ba.
Har ila yau kungiyar ta bukaci gidan sarautar Bahrain da ta mutunta hakkin furta albarkacin baki da duk wani yunkurin ‘yan adawa ta lumana tare da kawo karshen dokokin da suka hana kafa kungiyoyi da jam’iyyun siyasa a kasar.
Tun a ranar ashirin da takwa ga watan Disamban shekarar da ta gabata ta dubu biyu da sha hudu ahukuntan Bahrain suke tsare da Sheikh Ali Salman saboda furta rashin amincewarsa ga munanan matakan da ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ke dauka kan ‘yan adawan Bahrain.
3338629