Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na TRT na kasar Turkiya cewa, wani dan kunar bakin wake da ake zaton dan kungiyar boko Haram ne ya kai hari a kasuwar wani kauye dake jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
Wannan lamari ya auku ne a kauyen Rimirgo da ke karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nigeria inda rahoton ke cewa wani dan harin kunar bakin wake da ake kautata zaton dan kungiyar boko haram ne ya tayar da jikidar bama- bamai da ke daure a jikinsa a wurin binciken ababen hawa na hadin gwiwa tsakanin 'yan Kato da gora da jami'an tsaro da ke farkon shiga kauyen.
Babu wani mutun da ya rasa ransa sanadiyar harin baya ga dan kunar bakin wake, saidai wani dan kato da gora tare da wasu mutane biyu sun ji rauni.
Wannan Harin na zuwa ne a daidai lokacin da mai baiwa shugaban Nigeria shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno ya jagoranci manyan hafsan Sojin kasar zuwa jihar Borno, a wani mataki na tabbatar da umarnin da shugaba Muhammadu buhari ya ba rundunar sojin kasar da su kawo karshen kungiyar Boko Haram cikin watanni uku masu zuwa.
3344811