IQNA

‘Yan Ta’addan Daesh Sun Sake Yin Barazanar Rusa Dakin Ka’abah

23:55 - August 25, 2015
Lambar Labari: 3351571
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin fitatun ‘yan ta’addan kungiyar Daesh yay i barazanar cewa za su rusa dakin Kaba’a saboda mutane suna bauta masa koma bayan Allah.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga Bawabah News cewa, wani daya daga cikin fitatun ‘yan ta’addan kungiyar Daesh ya yi barazana shafinsa na twitter cewa za su rusa dakin Kaba’a saboda mutane suna bauta masa koma bayan Allah wanda hakan hada bauta ne, kamar yadda shi ma shugaban ‘yan ta’adda Abubakar Bagdadi ya yi wannanbarazana a lokutan baya.

Abu Turab Almaqdisi daya daga cikin fitattun yan ta’addan kungiyar Daesh y ace musulmi sun kafirta a lokacin da suka dauki dakin Ka;abah a amatsayin bauta, kuma abin takaici yanzu wasu msuulmin suna bauta ma wannan daki ne maaimakon Allah madaukakin sarki.

Ya ce suna gurin rusa wannan daki domin tsarkake bauta ga Allah, domin wannan daki ba komai ba ne ila duwatsu da aka tayar da gini da sub a su da wani matsayi da suka cancanci bautar musulmi

Tun shekarun baya shugaban yan ta’adda Abubakar Albaghdadi ya yi irin wannan barazana da ke cewa za su shiga Saudiyyah, kuma za su rusa dakin ka’aba wanda ake yin hirya  agefensa da suna aikin haji ko umra koma bayan Allah.

Al’ummar musulmi dai na cikin halin rashin tabbas kasantuwar wadannan mutane suna nan a cikin malamai da jami’ai a kasar saudiyya kuma za su iya aikata komaia  a lokacin da suke kara karfi.

3351440

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha