IQNA

Azhar Bata Amince Da Hankoron Yahudawa Na Raba Masallacin Aqsa Ba

23:52 - September 08, 2015
Lambar Labari: 3360643
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Tayyib sheikhul Azahar ya bayyana rashin amincewa dangane da yunkurin yahudawa na neman raba masallacin Aqsa da bagiransa.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-dastur cewa, Ahmad Tayyib a lokacin ya gana da Mahmud Alhabbash wakilin shugaban palastinawa Mahmud Abbas ya bayyana rashin amincewa dangane da yunkurin yahudawa na neman raba masallacin Aqsa da bagiransa na yanzu kuma na asali.

Tun da jijifin safiya jami’an tsaron yahudawan sahyuniya suka kaddamar da farmaki kan wanann wuri mai matsayi a wajen musulmi inda suka mamaye wani bangare na makabartar a wani mataki na tsokanar mabiya addinin muslunci kamar dai yadda suka saba yi a lokutan baya.

Manufar yahudawan sahyuniya ta yin hakan dai ita ce kokarin mamaye wurare mallakin musumi musamman ma wurare da mabiya addinai na muslunci da kiristanci suke girmamawa, domin mayar da su karkashin su ko kuma rusa su kowa ya rasa baki daya.

Dangane da haka ne kwamitin da ke kula lamurran mabiya adinan muslunci da kiristanci a birnin na Quds ya fitar da bayani a yau, inda ya yi Allawadai da akkakusar murya kan wannan mummunai aiki na tsokana, tare da yin kira ga gwamnatin yahudawan da ta kiyaye hakkokin addinai da aka safkar daga sama.

Shi dai wannan kwamitin ya tababtar a cikin bayanin da ya fitar cewa makamabartar Babu Rahma ta musulmi ce tantagarya, kuma keta alfarmar wannan wuri daidai yake da keta alfarmar wurare masu tsarki na mabiya addinin kiristanci da ke yankin a tarihi.

Shugaban kwamitin musulmi da kiristoci na birnin Quds ya bayyana cewa, wanann bas hi ne karon farko da yahudawan sahyuniya suka aikata irin wannan tabargaza ba, domin kuwa a lokutan baya sun mamaye kimanin mita dari takwas daga cikin wannan makamabrtar.

3360465

Abubuwan Da Ya Shafa: aqsa
captcha