Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na İslamazeri.az cewa, hukumar da ke kulak are kundin tsarin mulkin kasa a Jamus ta bayar da rahoton cewa yanzu haka wahabiyawa masu dauke da mmmunar akidar nan ta kafirta musulmi sun fara farautar wasu daga cikin musulmi masu gudun hijira a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wadanann wahabiyawa suna kokarin kara fada ayyukans tun bayan da ‘yan gudun hijirar suka fara fantsama a cikin kasashen turai, inda suke yin amfani da makudan kudade domin wanke kwakwalen wasu daga cikin ‘yan sunna da ke cikin yan gudun hijirar domin kafa wata kungiya tasu.
Tun kafin wanann lokacin wannan hkuma ta yi gargadin cewa ya zama wajibi kan mahukuntan kasar Jamus da su dauki matakan hana yaduwa ayyukan kungiyoyin wahabiya yan salafiya, domin kuwa su ne amsu tallar akidar ta’addanci, kuma hakan yana tatatre da hadari ga kasar.
3365298