IQNA

An Mika Wani Dan Alkaida Ga Kotun manyan laifuka Ta Duniya Kan Rusa Wuraren Tarihi A Mali

23:05 - September 26, 2015
Lambar Labari: 3370945
Bangaren kasa da kasa, kotun manyan laifuka ta duniya ta karbi wani dan Alka’ida bisa zarginsa da rusa wuraren tarihi a garin Timbuktu na kasar Mali domin hukunta shi.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Guradina cewa, kakakin kotun manyan laifuka ta duniya ya bayyan acewa, mahukuntan jamhuriyar Nijar suka mika mutumin mai suna Ahmad faqih Mahdi, wanda aka fi sani da Abu Turab.

Wanda shi ne mutum na farko da ya shiga hannun koun manyan laifukan yaki da duniya, bisa zarginsa da rusa muhimman wuraren tarihi na kasar Mali, da suka hada da tsoffin cibiyoyin ilimi da tarihi littafai da kuma kabrukan salihan bayi.

Tun a cikin watan Maris na shekara ta 2012 ne dai ‘yan alkaida suka kaddamar da hari a arewacin kasar Mali tare da kwace iko da yankin baki daya, inda suka yi ta rusa wuraren tarihi da cibiyoyin ilimi da aka gina daruruwan shekarda suka gabata.

Tun a kwanakin baya ne aka fara batun mika duk wadanda suke da hanu a wanann ta’asa da aiki na ta’addanci domin hukunta su a gaban kotun , wadda a halin yanzu ta bayyana shirinta na yin hukunci kan hakan.

‘yan ta’addan sun rusa muhimman wurare fiye da 10 a wannan gari wanda ya shahara da tsohon tarihinsa a kasar, kamar yadad kuma suka kafa dokokinsu an ta’addanci kan al’ummar yankin.

3370659

Abubuwan Da Ya Shafa: icc
captcha