IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Yi Allawadai Da Cin Zarafin Manzo A Danmark

23:24 - September 30, 2015
Lambar Labari: 3375976
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kakkausar da yin Allawadai da abin da ya faru na cin zarafin manzon Allah (SAW) a birnin Kopenhegen na kasar Danmark.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habrta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Abdulaziz Usman Tuwaijari babban sakataren kungiyar ta kasashen msuulmi, ya yi kakkausar da yin Allawadai da abin da ya faru na cin zarafin manzon Allah (SAW) ta hanyar zanen batunci a birnin Kopenhegen na Danmark a wannan mako.

Jami’in ya ci gaba da cewa abin mamamki ne yadda kasashen turai suke bayar da dama domin cin zarafin addinin muslunci da sunan yancin fadar albarkacin baki, alhali kuwa wannan cin zarafin akidar wasu mutanen ne masu yawa  aduniya su ne musulmi.

Al-tuwaijari ya ce ci gaba da aikata irin wannan mumunan aiki ba abu ne da musulmi za su amince da shi ba, kuma za a ci gaba da daukar matakai na ganin an kalu balance wannan akida takin jinin muslunci ta hanyoyi da suka dace wadanda za a dauka.

Da ma dsai hakan ba shi ne karon farko da masu kiyayya da addinin muslunci a kasar ta Danmark suke gudanar da irin wadannan taruka na cin zarafin addinin muslunbci ba.

Tun shekarun da suka gabat sun sha gudanar da irin wannan taro tare da gayyatar wasu masu irin akidarsu domin bata muslunci a nahiyar trai da duniya.

Su dai wadannan mutane manufarsu ita ce tsokanar musulmi tare da kokarin haddasa fito na fito tsakaninsu da sauran musulmi, ta yadda za su cimma burinsu a saukakae bata musulmin.

3375867

Abubuwan Da Ya Shafa: isesco
captcha